'Gawawwaki warwatse a kan tituna a Bama'

Hakkin mallakar hoto AFP BOKO HARAM
Image caption 'Yan Boko Haram sun kama 'yan civilian JTF a wani hari a Borno

Dan majalisar dattawa daga jihar Borno a Nigeria, Sanata Ahmad Zanna ya shaida wa BBC cewa gawawwaki na nan warwatse a kan tituna a garin Bama kwanaki biyu bayan 'yan Boko Haram sun kwace iko da garin.

A cewarsa, 'yan Boko Haram na sinturi a kan titunan garin Bama abinda ya hana mazauna garin yin jana'izar mutanen da suka mutu.

Bayanai sun nuna cewar dubban mazauna garin Bama sun tsere zuwa Maiduguri sakamakon hare-haren da 'yan Boko Haram suka kaddamar a garin.

Sai dai gwamnatin Nigeria ta karyata rahotannin da ke cewar garin Bama na karkashin ikon Boko Haram.

Sanata Zanna ya bukaci gwamnatin Nigeria ta tura karin sojoji Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno domin kare birnin daga harin 'yan Boko Haram, yana gargadi da cewa idan ba a dauki wannan matakin ba, to ba za ji dadin abin da zai biyo baya ba.

Hukumomi a jamhuriyar Kamaru sun ce yanzu haka 'yan gudun hijira fiye da 30,000 ne suka shigo kasar daga Nigeria sakamakon rikicin Boko Haram.

A yanzu haka dai 'yan gudun hijirar na zaune a wasu makarantu a yayin da wasu kuma suke zaune a karkashin bishiyoyi.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service