Ebola: Mutane fiye da 1900 ne suka mutu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutane sun mutu sosai a makonni ukun da suka gabata

Shugabar kungiyar lafiya ta duniya WHO Margaret Chan, tace mutane fiye da 1,900 ne a yanzu aka san sun mutu bayan barkewar cutar ebola a yammacin Afirka.

Kungiyar WHO tace kashi 40 cikin 100 na mace -macen da aka samu sun auku ne a makonni ukun da suka gabata.

An bada rahotan cewa mutane kusan 3,500 ne suka kamu da cutar ta ebola a kasashen Guinea da Saliyo da kuma Liberia.

Don haka Kungiyar WHO tace ana bukatar akalla dala miliyan dari -shida domin yaki da annobar