Kotu ta haramta Uber a Jamus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kamfanin ya ce ba zai dakatar da aikin sa ba

Wata kotu a Frankfurt ta haramta amfani da wata manhaja a wayoyin salula da ake amfani da ita wajen kiran motocin haya a daukacin Jamus.

Kotun ta yanke hukuncin cewa kamfanin ba shi da hurumin aiki a karkashin dokar Jamus.

Ta bayyana cewa an fadawa kamfanin a makon daya gabata cewa ba zai iya cigaba da aiki ba kuma za a ci tarar sa idan har yai kunnen kashi.

Amma wani mai magana da yawun Uber yace kamfanin ya yanke shawarar cewa ba zai dakatar da aikin sa ba.

Yana mai cewa haramcin ba zai yi aiki ba alhali an daukaka kara.

Jamus na daya daga cikin Kasashen duniya da suke da bunkasar cigaban kasuwar Uber a Turai in ji shi.

Jami'in ya kara da cewa 'Ba zaka iya takawa aikin birki ba. Uber zai cigaba da gudanar da aikinsa'.

Wani bincike da aka gudanar a manhajar kamfanin ta tabbatar da cewa direbobi sun cigaba da gudanar da aikinsu a Munich da Berlin da Hambur da Frankfurt da kuma Dusseldorf.

UberPop wanda aka kaddamar tunda fartkon wannan shekarar ya kuma dauki direbobi wadanda ba ma'aikatan kamfanin bane kai tsaye, kuma shekarunsu sun haura 21, suna kuma amfani da motocin kansu domin daukar fasinja.