Baidu ya kirkiro wani tsinken cin abinci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsinken yana gane abinci mara kyau

Kamfanin Baidu ya kirkiro da wani tsinken cin abinci da yake amfani da lantarki wanda zai iya tantance ko abinci ba shi da kyau.

Kamfanin ya ce tsinken cin abincin ka iya gano man girkin da ba shi da kyau, wani batu da ake damuwa da shi a Kasar.

A taron da ya sana gudanarwa shekara shekara a Beijing, kamfanin Baidu ya kuma kaddamar wani abin sauraron sauti da ake makala shi a ka, wanda zai yi gogayya da na Google.

Har yanzu dai abubuwan guda biyu ba su shiga hannun jama'a ba kuma kamfanin bai bayyana ranar da zai soma saida su ba.

Abin da ake amfani da shi wajen saurarar sauti na kamfanin Baidu na aiki ba tare da nuna hoto ba.

A wani bidiyo da aka nuna kan yadda tsinken cin abincin yake aiki, Baidu ya nuna tsinken yana auna zafin abinci da kuma sinadaran dake cikinsa