Watanni biyu babu wutar lantarki a Maiduguri

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jihar ta Borno dai ta shafe watanni fiye da 2 babu wutar lantarki.

Gwamnatin Jahar Borno a Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai yi aikin maido da hasken wutar lantarkin da aka shafe kusan watanni biyu babu a wasu bangarorin jahar da kuma Maiduguri babban birnin Jahar .

Wannan ya biyo bayan lalata Layin samar da hasken wutar lantarkin da 'yan bindiga suka yi a garin Damboa a irin hare haren da suke kaiwa, inda jihar ta kasance cikin rashin wuta na tsahon watanni biyu.

Kwamitin dai yace yana saran daga nan zuwa wata 1 zuwa 2 wutar Lantarkin zata samu .

An samu wannan tsaiko na gyaran wutar ne sakamakon ci gaba da kaddamar da hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kai wa a wasu yankuna na jihar ta Borno.

Kafin lalata wutar lantarki a wasu sassan jihar Bono, kungiyar a baya ma ta turbude wasu taga cikin turakan kamfanonin sadarwa a jihar.