Kare a Amurka ya cinye safuna 43

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Karen yana sha'awar sansana safa

Wani Kare ya farfado daga aikin tiyatar da akai masa na gaggawa a Amurka- wanda likitoci suka cire masa safuna 43 da rabi daga cikinsa.

Masu karen mai nauyin kilo 64, sun kwana da sanin cewa Karen -nasu yana son sansana safa, amma basu fahimci cewa yana lakume su a cikinsa ba.

Likitocin sun ce wadannan sune safuna mafi yawa da suka taba- cirewa wata dabba daga cikinta.

Sai dai sunce a wani lokaci an taba samun wani kwado daya cinye wasu duwatsun ado fiye da Talatin