Gonar Masara
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Matsalolin aikin noma a Afrika

Hakkin mallakar hoto Getty

Alkallumma na nuna cewa kimanin mutane miliyan biyar ne yunwa ke kashewa a Afrika a duk shekara, yayinda wasu miliyan dari-biyu ke fama da cututtuka masu nasaba da karancin abinci.

A watan Yunin da ya wuce, kasashen Afrika sun kuduri aniyar ninka yawan abincin da ake nomawa a nahiyar da kuma rage talauci kafin shekarar 2025.

Kuma jiya alhamis ne masana daga haniyar Afrika suka kammala wani taro a Ethiopia domin ganin yadda za a aiwatar da kudirin shugabannin kasashen Afrikar na inganta harkar noma.

To ko yaya matsalar take a zahiri? Wadanne matsaloli manoma ke fuskantar kuma ta yaya za a taimaka masu?