Mutane shida sun mutu a Gombe

Ambaliyar Ruwa
Image caption Gidaje sun rushe sakamakon ambaliyar Ruwa

Hukumomi a jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane akalla shida da kuma rushewar dimbin gidaje sanadiyar ambaliyar ruwa da aka fuskanta a jihar.

Lamarin dai ya faru ne da yamamcin ranar Jumma'a sanadiyar ruwan sama kamar da bakin kwarya abin da ya haifar da ambaliyar da kuma karyewar wata gada da ke kan hanyar Bauchi zuwa Gombe.

Lamarin da ya haddasa bacin rai da damuwa fa matafiyan da ke bin hanyar.

Wani mazaunin garin ya ce yawancin wadanda gidajensu suka rushe sakamakon ambaliyar, sun koma gidajen 'yan uwansu.

Bayanai dai na cewa, kimanin shekaru goma ke nan rabon birnin na Gombe da fuskantar irin wannan ta'adi, sai dai kuma an alakanta wannan lamari da rashin wadatattun magudannan ruwa da kuma toshewar wadanda ake da su.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba