Motorola ya fitar da sabon agogon hanu

Hakkin mallakar hoto AP

Kamfanin Motorola dake karkashin Google ya soma sayar da sabon agogon hanu da aka yi wa lakabi da Moto 360.

Kamfanin ya yi ammanar cewa agogon hanun zai ja hankali mutane saboda yadda aka kera shi .

Sabon agogon da aka kaddamar na zuwa ne a dai dai lokacin da kamfanin ke gudanar da sauye sauye domin bunkasa kasuwancisa.

A yanzu ne cinikin wayoyin tafi da gidanka na Motorola suka soma farfodawa kuma kamfanin na gab da komawa karkashin Lenovo bakidaya.

Sai dai ya yinda masu sharhi suka nuna kwarin gwiwa akan agogon ,sun kuma nuna shaku kan yuwuwar kasancewar agogon a matsayin agogon da ya fi kowane fice.

Motorola dai ya kaddamar da sabbin wayoyin tafi da gidanka da kuma wata naura da ake makalawa a kune da ake kira bluetooth earbud a turance .

Shugaban kamfanin, Rick Osterioh ya ce an inganta agogon fiye da sauran da aka kirkiro a baya.

Ya kuma amince cewa agogon baya da aka fitar zuwa wasu kasashe ba su da inganci.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Mr Osterioh ya ce sun rika samun korafi da ga wurin mutane game da fasalinsu.

Ya kuma yi marhaban akan yuwuwar shigowar kamfanin Apple cikin harkar a makon gobe.

Wani bincike na baya bayanan ya nuna cewa wayoyin Motorola na samun karbuwa sosai a India, abin da kuma ya sa ya sha gaban Nokia wajen komawa kamfanin waya na hudu da aka fi sayan wayoyinsa.

Haka kuma hannayen jarin kamfanin a Birtaniya sun tashi daga kashi 0.3 a shekarar 2012 zuwa kashi 5.2 a shekarar da muke ciki.