Maniyyatan Najeriya sun fara isa Saudia

Hakkin mallakar hoto AFP

Tawagar farko ta 'yan Najeriya daga Jihar Jigawa ta sauka a kasar Saudiya domin gudanar da aikin hajjin bana.

Hukomomi a Najeriya sun ce tuni alhazan suka fara isa masaukansu.

A jiya ne aka kaddamar da jigilar maniyyata aikin hajjin bana daga Najeriya zuwa kasa me sarki, inda ake sa ran kimanin mutane dubu 76 za su sauke farali a bana.

An dai kaddamar da fara jigilar ne a sabon filin jirgin sama na Dutse dake jihar Jigawa dake arewa maso yammacin kasar.

Sai dai gabanin fara tashin alhazan, hukumomin kasar sun yi barazanar dakatar da duk wani maniyyaci da ake da shakku game da ingancin lafiyar sa, dan gudun kada ya tafi da wata cuta da zai iya yadawa a kasar ta Saudia.