Congo ta doke Nijeriya 3-2

Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rabon da a ci Nijeriya a gida a wasa makamancin wannan tun shekaru 33 da suka wuce

Congo Brazzaville ta doke Nijeriya da ci 3-2 a wasan neman shiga gasar cin kofin Afrika da suka buga a birnin Calabar a rukunisu na farko.

Wannan shi ne karon farko cikin shekaru 33 da Super Eagles ta sha kashi a wasa mai zafi makamancin wannan a cikin gida.

Nijeriya dai ita ce ke rike da kofin gasar a yanzu haka.

Masana harkokin wasan kwallon kafa da dama na danganta wannan mamaya da Nijeriyar ta sha kan rikicin shugabanci da ya addabi hukumar kwallon kafar kasar.

Sauran wasannin da aka buga a nahiyar ta Afrika a wasannin neman shiga gasar a ranar Asabar, Cape Verde ta bi Niger har gida ta doke ta da ci 3-1, ita ma DR Congo da ta karbi bakuncin Kamaru ta sha kashi da ci 2-0.

Har ila yau Algeria ta bi Ethiopia har gida ta doke ta da ci 2-1 yayin da Zambia da Mozambique suka tashi canjaras, 0-0.