Za'a hana mutane fita a kasar Saliyo

Jammin ma'aikatar kiwon lafiya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jammin ma'aikatar kiwon lafiya

Gwamnatin Saliyo za ta kaddamar da shirin hana zira-zirga a fadin kasar na tsawon kwanaki hudu domin dakile yaduwar cutar Ebola.

Wani babban jami'i a offishin shugaban kasa ya ce za a hana mutane fita daga gidajensu daga ranar 18 zuwa 21 na watan mu ke ciki.

Matakin da mahukunta Saliyo suka dauka na zuwa ne a dai dai lokacinda Hukumar lafiya ta duniya ta ce za'a iya amfani da jinin mutane da suka warke daga cutar ebola wajen yi wa mutanen da suka kamu da cutar magani.

Kwararu akan kiwon lafiya da suka yi taro a Geneva sun ce me yu wa kwayoyin garkuwa jiki dake cikin jinin wadanda suka warke su taimaka wa wadanda ake yi wa jinya samun sauki ,

Cutar ta hallaka mutane fiye da dubu 2 a kasashen Saliyo da Liberia Guinea da kuma Nigeria tun bayan bular ta a watan Maris daya gabata.