Al shabab ta nada sabon shugaban kungiyar

Mayakan kungiyar Al shabab Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan kungiyar All shabab

Kungiyar Al shabab mai kaifin kishin islama a Somalia ta tabbatar da mutuwar shugabanta Ahmed Abdi Godane kuma ta bayana Sheik Ahmad Umar a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

Ba bu cikakaken bayani akan mutumin da aka nada a matsayin sabon shugaban kungiyar Al shabab watau Ahmed Umar da aka fi sani da Abu Obaida.

Ya dai karbi jagorancin kungiya ne bayan kisan da aka yi wa shugaban kungiyar watau Godane a harin ta sama da Amurka ta kai a yankin kudancin Somalia.

An kuma kashe kwamadojin kungiyar su biyu a harin .

Sai dai ya yinda kungiyar Al shabab ba ta bata lokaci ba wajen zabar wanda zai maye gurbin Godane za'a iya cewa kungiyar ta nuna alamun za ta cigaba da kai hare hare ba bu kakkautawa.