Ukraine: Tsagaita wuta na aiki

Hakkin mallakar hoto AFP

Shugabannin kasashen Rasha da Ukraine sun ce sun gamsu yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a gabashin Ukraine ta na aiki.

Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Ukraine Petro Proshenko sun tattauna tsagaita wutar ta wayar tarho kwana guda bayan cimma yarjejeniyar.

Bangarorin biyu sun jaddada muhimmancin sa ido na tawagar kasa da kasa da kuma raba kayan agaji.

Sai dai kungiyar agaji ta Red Cross ta ce tun da farko a yau an tilastawa wasu daga cikin motocinta dauke da kayan agaji da suka nufi birnin Luhansk da ke hannun yan aware dawowa saboda luguden wuta.

Karin bayani