Kasashen larabawa za su yaki IS

Hakkin mallakar hoto AP

Ministocin harkokin wajen kasashen larabawa sun amince za su dauki dukkan matakan da suka zama wajibi wajen tunkarar mayakan kasar musulunci.

Haka kuma sun amince su hada hannu da sauran kasashen duniya domin yin maganin yan tawayen.

Taron wanda suka gudanar a birnin Alhakira ya kuma jaddada goyon baya ga kudirin da kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya zartar a watan da ya gabata wanda ya bukaci mambobin kasashe su dakatar da bada taimakon sufuri da makamai da kuma kudade ga masu tsatsaurar ra'ayi a Iraqi da kuma Syria.

Tun da farko sakatare janar na kungiyar kasashen larabawa Nabil El Arabi yace abin da ake bukata a yanzu shine daukar kwararan matakai na karfin soji da siyasa da kuma na tattalin arziki.

Yace abin da ke faruwa a Iraqi shine kungiyar yan ta'addar bama suna kalubalantar gwamnatin ba ne kadai suna ma barazana ga dorewar kasar da kuma sauran kasashe.