Shugaba Jonathan zai kai ziyara Chadi

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

A yau ne shugaban Nigeria Goodluck Jonathan zai ziyarci birnin Ndjamena na kasar Chadi don tattaunawa da shugaban kasar Idriss Deby kan sha'anin tsaro tsakanin kasashen biyu.

Fadar shugaban kasa ta ce shugabbannin biyu zasu ci gaba da tattaunawa akan matsayar da suka cimma a taron shugabannin kasashen Afrika suka yi a kan sha'anin tsaro a makon daya gabata a Kenya.

Gwamantin Najeriya ta ce shugaba Jonathan tare da takwaran sa na kasar Chadi Idriss Deby za su maida hankali kan hanyoyin da ya kamata abi na aiwatar da yarjejeniyar hadin kai wajen yaki da ta'addanci a yankin

Nigeria da Chadi da Niger da kuma kasar Kamaru sun amince su hada karfi da karfe wajen yaki da ta'adanci a taron da suka gudanar a birnin Paris a farkon wannan shekarar.