Nigeria na jiran hukuncin Fifa

Idan haramcin ya tabbata, Zakarun Afirkan ba za su iya buga wasansu na zuwa gasar cin kofin Afirka ba.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Idan haramcin ya tabbata, Zakarun Afirkan ba za su iya buga wasansu na zuwa gasar cin kofin Afirka ba.

Nijeriya na jiran hukuncin karshe na dakatarwa daga harkokin kwallon kafar duniya bayan cikar wa'adin Hukumar Fifa da safiyar Litinin, karfe 7 agogon GMT.

Hukumar kwallon kafa ta duniya ta bai wa Chris Giwa lokaci, don ya yi watsi da ikirarin kasancewa shugaban Hukumar kwallon Nijeriya NFF.

Fifa ta ba da wa'adin ne a makon jiya, inda ta jaddada cewa ba ta amince da zabensa na ranar 26 ga watan Agusta ba.

Sai dai, Chris Giwa ya dage cewa ba zai sauka daga mukaminsa ba, duk da bukatar hakan da Fifa ta yi.

Hukumar Fifa ta ce tana iya dakatar da hukunci, idan aka dawo da shugabancin Hukumar NFF kamar yadda yake ranar 25 ga watan Agusta, tare da Aminu Maigari a matsayin shugaba.

Fifa ta kuma bukaci wani sabon kwamitin Hukumar ya gudanar da zaben ba tare da bata lokaci ba.

Kwamitin gaggawa na Hukumar Fifa ne ya ba da wa'adin karshe, ranar Laraba bayan wa'adin 1 ga watan Satumba ya wuce, ba tare da Giwa ya sauka ba.