Amurka ta amince da sabuwar gwamnatin Iraki

Image caption Mr. Kerry ya ce akwai bukatar kasashen duniya su taimaka wajen dakile ayyukan kungiyar IS

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya yi maraba da sabuwar gwamnatin hadakar da aka kafa a Iraki.

A ranar Litinin ne majalisar dokokin Irakin ta amince da gwamnatin hadin gwiwa tsakanin 'yan shi'a da Sunni masu rinjaye da kuma Kurdawa, a karkashin jagorancin Firai minista Haidar al-Abadi.

Mr. Kerry ya kwatanta lamarin a matsayin muhimmin mataki da zai kawo karshen ayyukan mayakan kungiyar da ke fafutukar kafa daular Muslunci.

Sakataren Amurkan zai yi tafiya zuwa Saudiya da kuma Jordan a makon da muke ciki, a yunkurin da Amurka ke yi na kafa rundunar tsaro ta hadin gwiwa da za ta tunkari kungiyar da ta mamaye manyan yankuna a Iraqi da kuma Syria.

Karin bayani