Apple ya dauki Newson a aiki

Apple Hakkin mallakar hoto Xinhua
Image caption Masana na hasashen cewa Apple zai fara kera wasu kayayyaki baya ga wadanda ya saba

Rahotanni sun ce kamfanin Apple ya dauki shahararren mutumin nan mai tsara agogo, Marc Newson a aiki.

Mr. Newson wanda ya yi fice a fannin tsara agogon hanu ya kasance mutum fitacce na baya bayan nan da ya fara aiki da Apple, duk da cewa a baya, ya yi wasu ayyuka da kamfanin.

Wannan lamari ya kuma sa masu sharhi a fannin kere-keren na'urorin zamani suka fara hasashen cewa watakila kamfanin na Apple zai fara tunanin bullo da wasu kayayyaki ne baya ga samar da na'urorin zamani.

Babban mai kula da sashen fannin tsare-tsare na kamfanin Apple, Jonathan Ive, wanda kuma aboki ne ga Newson, ya kwatanta shi a matsayin mutum mai "basira ta daban".

Newson ya nuna matukar farin cikinsa kan fara aiki da Apple, "ina mai cike da alfahari" da fara aiki da Apple.

A baya Newson ya tsara kayayyaki da dama da suka hada da kayyakin kujeru da tufafi da kuma agogon hanu.

Duk da cewa Apple ta dauki Newson ne domin ya mayar da hankali kan tsara wasu kayayyaki na musamman, akwai yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu na cewa Newson zai dinga yin wasu ayyukan kansa na daban da basu shafi Apple ba.

Zai kuma dinga gudanar da ayyukan nasa na kansa ne daga ofishinsa dake London.