Ebola: AU na so a cire haramcin tafiye-tafiye

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taron na ranar Litinin ya ce haramcin zai iya shafar tattalin arzikin nahiyar

Kungiyar tarayyar Afrika ta yi kira da a cire haramcin da aka sanya game da tafiye-tafiye zuwa kasashen da ke fama da cutar Ebola.

A wani taron gaggawa da kungiyar ta yi a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia, kungiyar ta ce haramcin zai iya janyo tsangwama ga masu fama da cutar da kuma kasashensu.

Hakan na zuwa ne yayin da Hukumar Lafiya ta duniya ke nuna fargaba game da yiwuwar samun wasu dubban mutanen da za su iya kamuwa da cutar a makonni masu zuwa a yammacin Afrika.

Kungiyar agajin likitoci ta MSF ta ce yawan masu fama da cutar Ebola a Liberia na son ya fi karfinta.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba