Ebola:Hukumar lafiya ta gargadi Liberia

Ma'aikatan lafiya Hakkin mallakar hoto na
Image caption Ma'aikatan lafiya

Hukumar lafiya ta duniya ta gargadi Liberia akan za'a samu karuwa a yawan mutane da suka kamu da cutar Ebola a kasar a 'yan makonni masu zuwa.

A cikin wata sanarwa da Hukumar ta fitar ta ce cutar na yaduwa fiye da yadda ake tunani a Liberia , inda ta hallaka mutane fiye da duba daya.

Ta ce ana kyautata zaton direbobin taxi da kuma yan achaba na cikin wadanda ke yada da cutar.

Kungiyar tarayyar Afrika ta yi kira ga mambobinta akan kada su haramtawa mutane tafiye tafiye zuwa kasashen dake fama da cutar saboda hakan kan iya janyo tsangwama da kuma cikas ga tattalin arzikin nahiyar.