An nanata kira game da jirgin saman Malaysia

Jirgin sman Yukuren
Bayanan hoto,

A bar masu bincike su yi aikinsu

Kasashen Malaysia, da Australia da kuma Holland sun nanata kira ga bangaren gwamnatin Yukuren da kuma 'yan tawaye da ke fada da juna da su bari masu bincike su shiga wurin da jirgin saman Malaysia ya fadi.

Wani kwarya-kwaryan rahoton da masu binciken suka fitar ya nuna cewa jirgin ya fadi ne sakamakon harbinsa da aka yi.

Kwararru daga kasar Malaysia da kuma Holland sun je gabashin Yukuren ne don gano musabbabin faduwar jirgin, wanda ya yi sanadin mutuwar kusan mutum dari uku.

Firayim Ministan kasar Holland, Mark Rutte, ya ce masu bincike suna kokari ne su bankado gaskiyar abin da ya faru.

Ya ce ba za mu yi gaggawar yanke hukunci ba. kasar Holland ita ce ke jagorantar masu bincike. kwararru na aiki daki-daki ne da nufin raba-gardama.