Jama'ar Yola na zaman dar- dar

Wasu masu gudun hijira saboda rikicin Boko Haram Hakkin mallakar hoto Reuters

Jama'ar Yola, babban birnin Jihar Adamawa a Najeriya na zaman dar-dar yayinda Boko Haram ke cigaba da rike da wasu garuruwa a Jihar.

Michika, Bazza da Gulak na daga cikin garuruwan da har yanzu ke karkashin 'yan Boko Haram din.

Rohotanni sun ce jama'a na cigaba da kaura zuwa Yola daga wasu sassan jihar.

Yanzu haka dai gwamnatin Jihar ta bude wassu sansanoni domin bada kulawa ga masu gudun hijirar.

Wakilin BBC a garin Yola, Abdullahi Tasiu Abubakar ya ce: "jama'a da yawa na ficewa daga Yola, kuma wasu na cikin tashin hankali."

Jihar ta Adamawa dai na karkashin dokar ta baci tareda sauran jihohi a yankin arewa maso-gabashin Najeriya saboda rikicin na Boko Haram.

Karin bayani