'A cire kyallayen #BringbackJonathan2015'

Image caption Jonathan ya ce bada sanin sa ake yin kiraye-kitayen ba

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan ya ba da umurnin a cire kyallaye da hotuna masu nuni da maudu'in #BringbackJonathan2015 wadanda ke kira gare shi da ya ci gaba da mulkin Nigeria.

Matakin shugaban kasar, ya biyo bayan kakkausar sukar da yake sha a kafafen yada labarai da kuma shafukan zumunta na zamani game da wadannan kyallaye da ke kwaikwayon masu fafutukar ganin an ceto 'yan matan Chibok da ke amfani da maudu'in #Bringbackourgirls.

Image caption Jonathan ya sha suka game da allunan

Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar ta ce ba da izinin Shugaba Jonathan aka kafa kyallaye ba kuma matakin ya nuna rashin tausayi ga masu gangamin ganin cewar an ceto dalibai 'yan matan Chibok fiye da 200 da 'yan Boko Haram suka sace.

An kafa allunan #BringbackJonathan2015 ne dai a wurare da dama a Abuja babban birnin Nigeria wadanda ke kira gare shi da ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar a shekara ta 2015.

Sanarwar ta fadar shugaban kasar ta kuma tabbatarwa 'yan Nigeria da sauran kasashen duniya cewar, Mr Jonathan zai ci gaba da abubuwan da suka dace domin ceto 'yan matan Chibok daga hannun 'yan Boko Haram.