Ebola: Gwamnati za ta gurfanar da masu tsangwama

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mutane kalilan ne ke warkewa daga cutar idan aka kwatanta da wadanda suka mutu

Gwamnatin jihar Lagos ta umarci ma'aikatar shari'a ta jihar ta gurfanar da duk wanda ya tsangwami wadanda suka warke daga cutar Ebola.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Jide Idris ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a Lagos, inda ya nemi duk wanda aka tsangwama ya mika kokensa ga ma'aikatar shari'ar.

Hakan ya biyo bayan rahotannin da ke nuna cewa wasu mutane biyu da suka warke daga cutar Ebola na fuskantar tsangwama duk da cewa an tabbatar da koshin lafiyarsu.

Inda ya kara da cewa matakin kandagarki ne na kawar da yiwuwar boye masu cutar, abin da ka iya jefa iyalai da kuma al'umma cikin hatsarin harbuwa da cutar.

An kori daya daga cikin mutanen da suka warke ne daga gidan da yake haya, yayin da dayan kuma aka sallame shi daga aiki.

Karin bayani