An saci bayanai a kamfanin Target na Amurka

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Satar bayanai da aka yi a Kamfanin Target ta shafi mutane miliyan 70 masu mu'amalla da shi.

Barayi masu satar bayanai a internet sun yi kokarin kutsawa cikin tsarin nan na biyan kudi ta hanyar katin banki a kantunan kamfanin Target.

Kasaitaccen kamfanin na Target na Amurka ya ce an saci bayanai na katunan banki na abokan huddarsa kimanin miliyan 70 daga matattarar bayanai ta kamfanin a cikin watan Disamba - watau da karin wasu miliyan talatin sabanin alkaluman da ta bayar tun da farko.

Kamfanin na Target yace barayin sun saci lambobin katunan da sunayen mutanen masu katunan da lambar gidajensu da lambobin wayoyinsu da adireshinsu na email.

An fara satar bayanan ne a ranar ko wajajen 29 ga watan Nuwamba, ranar da aka kira bakar Jumma'a, watau daya daga cikin ranakun da aka fi cinikin kayayyakin kamfanin a shekara.

Kamfanin dai ya ce babu wani abokan huddarsa da zai yi hasara ko ta kwandala a kowacce irin zamba aka tafka sakamakon wannan satar bayanan.

To, amma wannan bai hana wasu abokan huddar ta sa gurfanar da kamfanin a gaban Kotu ba, inda suke ikirarin cewa kamfanin ya gaza sheida musu game da satar bayanan kafin a ba da rahoton ta, sannan kuma bai dauki kwarara matakan tsaro ba don kare satar.

Gregg Steinhafel Shugaban kamfanin na Target ya ce, "na san abin ban takaici ne ga abokan huddar mu su samu labarin cewa an saci wadannan bayanai kuma muna ba su matukar hakuri da suka jure wannan."

Kamfanin na Target ya yi tayin ba da kariya tare da sa ido ga huddodin kudi na abokan huddar sa a Amurka kyauta har tsawon shekara daya.

Brian Krebs mai bincike kan sha'an tsaro wanda ya yi rubuce-rubuce kan satar bayanan a watan Disamba ya ce wasu majiyoyi a kamfanonin dake tafiyar da huddar hada-hadar sayayya da katin banki sun shaida masa cewa barayin sun jefa wani tsari ne na satar bayanai a naurorin dake binciken katin biyan kudade a kantunan kamfanin na Target 1,797.

Barayin sun saci bayanan ne a tsakanin ranar hutu ta thanksgiving da 15 ga watan Disamba a cewar kamfanin na Target. Wadannan bayanan yawanci a kan sayar ma masu aikata miyagun laifukka ne ta kasuwar mazambata dake gudana a asirce.

Karin bayani