Bill da Melinda sun ba da tallafin Ebola

Likitocin da ke kula da masu dauke da cutar Ebola. Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hukumar lafiya ta duniya ta ce kawo yanzu cutar Ebola ta hallaka mutane fiye da 2000 a yammacin Afurka.

Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta ce za ta ba da tallafin dala miliyan hamsin domin yakar cutar Ebola da ta barke a yammacin Afurka.

Gidauniyar ta shahararren attajirin nan Bill Gates ta ce za ta ba da kudaden ba tare da bata lokaci ba ga kungiyoyin kasashen waje domin magance matsalar da ta kira ta gaggawa.

Dr David Nabarro wanda ke jagorantar kokarin da Majalisar Dinkin Duniya ke yi na dakile cutar ya shaida wa BBC cewa Cutar Ebola na kara kamari fiye da tunanin dan adam.

Susan Desmond- Hellman ita ce babbar jami'ar shirin tallafin ta kuma shaida wa BBC cewa ana bukatar karin kudade dan yakar cutar.

Inda ta ce ya kamata kasar Amurka da Tarayyar Turai da sauran kassahen duniya, su ma su ba da tallafi dan yakar wannan babbar annoba da ke barazana ga duniya ba ki daya.