Zan fi son shari'a a waje - Hama Amadou

Hama Amadou Shugaban Majalisar dokokin Nijer Hakkin mallakar hoto
Image caption Hama Amadou Shugaban Majalisar dokokin Nijer

A Jumhuriyar Niger shugaban majalisar dokokin kasar Malam Hama Amadu wanda ke kasar Faransa a yanzu haka, ya ce ya fi da son gwamnatin ta Nijar ta ba kasashen duniya izinin su kama shi.

Haka din zai ba shi damar kare kansa daga zargin da hukumomin na Nijar ke yi masa.

Malam Hama Amadun ya bar Nijar tun cikin watan da ya gabata don gudun kada ya gurfana gaban alkali bayan da kwamitin gudanarwa na majalisar dokoki ya cire masa kariya domin ya gurfana gaban alkali bisa zarginsa da hannu a safarar jarirai daga Nijeriya zuwa kasar ta Nijar.

Karin bayani