Za mu iya murkushe su - Tsoffin Sojoji

Tsoffin Sojan Nijeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tsoffin Sojan Nijeriya

A Najeriya, wasu tsofaffin sojoji a kasar sun ce inda gwamnatin kasar za ta biya su hakkokinsu, a shirye suke su taimaka wajen yakar 'yan kungiyar Boko Haram da suka addabi wasu jihohin arewa maso gabashin kasar.

Tsofaffin sojojin suka ce a yadda suke yanzu, ba sa jin tsoron mutuwa, kuma suna da dabaru da kwarewa ta samun galaba a kan 'ya'yan kungiyar.

Sojojin sun sanar da hakan ne yayin wata zanga-zanga da suka gudanar a Abuja don nuna rashin jin dadinsu da rashin biyansu wasu hakkokinsu.

Karin bayani