Mata a fannin mai na Nigeria

Maza ne suka yi kane-kane a fannin mai da iskar gas a Najeriya, kamar yadda bincike ya nuna cewa manyan dakunan taro na mafi yawan kamfanonin mai sun zamo tamkar majalisar maza.

Sai dai hamshakan 'yan kasuwa mata sun kuduri aniyar sauya hakan a kasar.

Ministar man fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke ta zama wata babbar jagora a gare su.

"A kashin gaskiya manyan mukamai na man fetur da na kudi mata ne ke rike da su a Najeriya, kuma hakan na nuna irin ci gaban da muka samu, Ministar na nuni da ministar kudi, Ngozi Okonjo-Iweala.

"Ba wai don kawai muna mata ba ne muke rike da mukaman, sai don kwarewarmu wajen gudanarwa." Ta bayyana haka a wani taro a Vienna.

Sai dai wasu bincike na nuna cewa har yanzu matan da ke rike da manyan mukamai ba su da yawa a kamfanonin mai da iskar gas a duniya.

Laura Manson-Smith ta kamfanin PricewaterhouseCoopers ta ce babu wani wakilci na mata a fannin.

"Ina mamakin karancin kason da mata daraktoci ke da shi a kamfanonin mai da iskar gas a fadin duniya, wato kashi goma sha daya cikin dari, kuma mafi yawansu suna rike ne da mukamai marasa girma, kashi daya ne cikin dari na manyan mukamai ke hannun mata."

Hako mai a tsakiyar teku

Najeriya ce kasa ta 14 mafi hako mai a duniya, inda take hako gangar danyen mai 2.4 miliyan a rana, kuma ta dauki matakan bude kofofinta na masana'antar mai ga 'yan kasar.

Kuma yanzu wasu hamshakan 'yan kasuwa mata na fatan yin amfani da wannan dama wajen kara yawansu a fannin.

"A lokacin da muka taso sunan kawai da muka ji ana kira shi ne Magret Thatcher". A cewar wata babbar darakta a kamfanin ayyukan mai na Ladol da ke jihar Lagos, Amy Jadesimi.

Dr. Jadesimi mai shekaru sama da talatin tsohuwar mai sharhi ga Goldman Sachs kuma likita ta ce a yau " Ana yi wa mata rikon sakainar kashi, duk da cewa mace za ta iya kaiwa kololuwar mukami a cikin al'umma."

Ladol ta mai da wata fadama da ake zubar da dagwalon masana'antu zuwa tashar jiragen ruwa da ta lashe $500 miliyan, domin taimaka wa ayyukan mai na cikin teku, kamar gyaran jiragen ruwa da sauran ayyukan kere-kere.

Kuma kamfanin na fatan fadada wajen ta hanyar zuba jari na dala biliyan daya.

Catherine Uju Ifejike ce shugabar wani gungun kamfanoni na mai da iskar gas na Britannia U Group.

Harkar da take jagoranta ta sayi hannayen jari na wani wurin hakar mai da iskar gas, Ajapa, wanda a cewarta ya ke da ma'adanin da ba a hako ba na kimanin $4.3 biliyan.

Cikin barkwanci ta ce "Ku maza ba ku iya tafasa ruwa ba, ballantana ma inda ake ajiyar kayan makarantar yara."

"Mun kula da gidajenku, kuma a yanzu mun fara yin haka ta hanyar rike ayyuka masu girma tare da mallakar kamfanoni. A cikin shekaru shida na kafa kamfanoni bakwai."

Ta ce kashi 70 cikin dari na ma'aikatanta maza ne "Kuma abu ne banbarakwai a gare su."