'Pistorius bai aikata kisa da gangan ba'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Oscar Pistorius ya fashe da kuka a cikin kotu

Mai shari'a Thokolize Masipa, wadda ke yanke hukunci a shari'ar da ake yi wa magujin nan dan Afrika ta Kudu, Oscar Pistorius ta ce ya yi ganganci, ya kuma yi amfani da karfin da ya wuce kima.

Ta dage zaman kotun sai kuma a gobe Juma'a ne, mai shari'a Masipa za ta yanke hukunci kan ko kotun ta samu Oscar Pistorius da laifin kashe buduwarsa, Reeva Steenamp ba da niyya ba.

Hakan na zuwa ne bayan da ta yi watsi da dukkan zargin aikata kisan kai da gangan.

Pistorius wanda ya fashe da kuka a ciki kotun, ya ce ba da gangan ya kashe Reeva Steenkamp.