Za a yanke wa Pistorius hukunci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Oscar Pistorius

Mai shari'ar da ke sauraren shari'ar da ake yi wa fitaccen dan wasan tsere Oscar Pistorius za ta yanke hukunci kan shari'ar da aka dauki lokaci ana gudanar da ita.

Mr Pistorius dai ya amince da harbe budurwarsa Reeva Steenkamp a gidansa da ke birnin Pretoria a shekarar da ta gabata, sai dai ya musanta aikata harbin da gangan inda ya ce ya dauka wani ne ya masa kutse dalilin da ya sa ya yi harbin kenan.

Sai dai masu shigar da kara sun ci gaba da nana ta cewar ya yi harbin ne da gangan, lamarin da ya janyo daukar lokaci ana musayar yawu daga bangarorin biyu.

Wakilin BBC Afirka na ganin cewa ta yiwu mai shari'a Thokozile Masipa ta kai har zuwa gobe juma'a kafin ta sanar da hukuncin da ta yankewa Mr Pistorius.

Haka kuma ta na sake nazari akan dukkan shaidu talatin da bakwai da aka gabatar ciki kuwa har da shi kansa Mr Pistorius din.