Obama ya ba da umarnin kai hari Syria

Shugaba Obama Hakkin mallakar hoto
Image caption Mr Obama yace matakin da Amurka za ta dauka wannan karo a kan kungiyar ISIL ya sha banban da wadanda aka dauka a kassahen Iraqi da kuma Afghanistan

A karon farko shugaba Obama ya ba da umarnin kaddamar da hare-hare ta sama a Syria a wani bangare na yakar masu ta da kayar baya na kungiyar IS.

A wani jawabi da ya gabatar ta kafafen talabijin Mr Obama ya yi alkawarin cewa za a fadada hare-hare ta sama da Amurka ke kaiwa akan masu tada kayar baya na kungiyar IS a Iraqi.

Da yake sanar da tsarin sa na yakar Is da aka juma ana jira, Mr Obama ya ce Amurka za ta jagoranci wani kawance dan yakar 'yan ta'addar da suke iko da wasu sassan kasashen Iraqi da Syria, inda a baya-bayan ann suka yanka wasu 'yan jarida Amurkawa su biyu.

Mr Obama ya kira kungiyar ta IS da cewa wata cutar daji ko Cancer amma yayi alkawarin daukar matakan murkusheta.

Yace za a dauki lokaci kafin ashawo kan cutar Daji kamar ISIL, kuma duk lokacin da aka dauki matakan soji, sai ka ga matakin na dauke da hadari ga dakaru maza da mata.

Amma wanna karon ya na son Amurkawa su gane banbancin wannan yakin da wanda Amurka ta yi a baya a kasashen Iraqi da Afghanistan.