'An kashe 'yan Boko Haram a Konduga'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau da mayakansa

Rundunar tsaron Nigeria ta yi ikirarin samun nasara a kan 'yan Boko Haram a garin Konduga da ke jihar Borno.

Hukumomin tsaro sun ce 'yan Boko Haram sun kaddamar da hari a garin Konduga da misalin karfe 4 na asuba a ranar Juma'a amma kuma sai aka katse hanzarinsu.

Dakarun Nigeria din sun ce bayan ba ta kashi na tsawon sa'o'i uku, sun samu damar kashe mayakan Boko Haram fiye da 100.

A cewar hukumomi a Nigeria, 'yan Boko Haram sun kaddamar da harin a cikin motoci kirar Hilux hudu da kuma manyan makamai.

Wani mazaunin garin Konduga ya shaidawa BBC cewar sojojin Nigeria sun kashe dukka mayakan Boko Haram din da suka kai hari a Konduga.

Garin Konduga na da tazarar kilomita 30 daga Maiduguri babban birnin jihar ta Borno.

A ranar Alhamis ne kungiyar dattawan jihar Borno ta yi gargadin cewar 'yan Boko Haram sun yi wa Maiduguri kawanya kuma idan ba a dauki mataki ba, to babban bala'i na nan tafe.