Rikici tsakanin Google da Tarayyar Turai

Kamfanin Google Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Kamfanin Google

Hukumar Tarayyar Turai tana neman wani sabon sassaucin daga kamfanin Google a kan yadda yake nuno sakamakon bincike a shafukkan internet.

Binciken wanda dadadde ne na da nufin magance wata damuwa da ake da ita kan cewar kasaitaccen kamfanin ya saba ma karbuwar da ya yi a kasuwar bincike ta tarayyar Turai.

Kwamishina mai kula da harkokin gasa na kungiyar Joaquin Almunia ya bayyana cewar zai kuma iya neman wani bahasin daga wani kamfanin da Google ke tafiyarwa Android.

Kamfanin na Google dai ya ce yana kokarin warware matsalar da hukumar tarayyar Turan.

Tun cikin shekara ta 2010 ake wannan takaddamar bayan wasu abokan hamayyar da suka hada da shafin internet na Brittaniya mai gwada bambancin farashin kayayyaki tsakanin kamfanoni watau Foundem wadanda suka yi koken cewa irin yadda Google ke nuna sakamakon bincike sam ba ya nuna gasa tsakanin kamfanoni.

A Tarayyar Turan kamfanin Google ne ya mamaye kashi 90 bisa dari na kasuwar bincike.

A wata yarjejeniya da aka kulla a cikin watan Febrairu, kamfanin Google ya amince zai kebe wani sashe a kusa da shafin bincike na Tarayyar Turai saboda masu gasa, wanda za a baiwa kamfanoni masu gasa tallatar da kayansu ta hanyar gwanjonsu.

Kamfanonin masu gasa sun ce gwanjon kayayyakin zai iya samar wa kamfanin Google kudin shiga da suka zarce euro miliyan dari ukku.

A karkashin tsarin na gwanjon kayayyakin Kamfanin Google zai samu karin kudin shiga masu yawan gaske. David Wood lauya mai wakiltar gamayyar wasu kamfanoni wadanda suka kunshi kamfanin Microsoft da Foundem ya ce "kamar a gaya ma dan fashi da makami ne cewar ba zai iya kara yin sata ba, to amma zai iya tarbe hanya a babban titin da ake hada-hada."

Ya kara da cewa abinda kawai kamfanin Google zai yi don warware matsalar shine amfani da wani lissafin ga wasu shafukkan na internet na wasu kamar dai yadda kamfanin ya yi ga wadanda ya mallaka.

Karin bayani