'Yan Boko Haram sun kai hari a Konduga

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bayanai sun ce sojoji sun katse hanzarin 'yan Boko Haram

Hukumomi a Nigeria sun tabbatar da cewar 'yan Boko Haram sun kai hari a garin Konduga da ke kusa da birnin Maiduguri a jihar Borno.

Kakakin cibiyar samar da bayanai ta gwamnatin Nigeria, Mike Omeri ya tabbatar da harin da aka kai a Konduga da misalin karfe 4 na asubahin ranar Juma'a.

Mazauna garin Konduga sun shaidawa BBC cewar mayakan Boko Haram sun shigo garin cikin manyan motoci da gab da Sallar asuba kafin dakarun Nigeria su katse musu hanzari.

Bayanai sun ce an kashe 'yan Boko Haram da dama sakamakon gumurzu da sojojin Nigeria wadanda suka hana su cin cimma burin da ya kai su Kondugan.

Garin Kondunga na da tazarar kilomita 25 daga Maiduguri babban birnin jihar ta Borno.

A ranar Alhamis ne kungiyar dattawan jihar Borno ta yi gargadin cewar 'yan Boko Haram sun yi wa Maiduguri kawanya kuma idan ba a dauki mataki ba, to babban bala'i na nan tafe.