Mutane 40 sun mutu a wani gini a Lagos

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Hukumomi a Najeriya sun ce yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon rushewar wani gini mallakar wani coci a birnin Lagos na kudu maso yammacin kasar ya kai 40.

Kakakin Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) shiyyar Lagos, Ibrahim Farinloye, wanda ya shaida wa BBC hakan, ya kuma ce ma'aikatan agaji sun yi nasarar zakulo mutane da dama a raye.

"A halin yanzu akwai mutane kusan 130 da aka ceto su da ransu; kuma ana ci gaba da aikin ceto saboda alamu na nuna cewa akwai wasu mutanen a cikin baraguzan ginin", inji Mista Farinloye.

A ranar Juma'a ne dai benen mai hawa shida, wanda cocin Synagogue Church of All Nations ke amfani da shi don saukar baki daga sassa daban-daban na duniya, ya rufta.

Ginin dai asalinsa bene ne hawa biyu, kuma ana cikin aikin kara masa hawa hudu ne ya fadi.

Daya daga cikin malaman addinin Kirista da suka fi shahara a Najeriya, T.B. Joshua, shi ne jagoran cocin da ya mallaki ginin.

Karin bayani