'Ba da gangan ba Pistorius ya yi kisa'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Pistorius ya fashe da kuka a cikin kotu

Kotu ta same dan tseren Afrika ta Kudu, Oscar Pistorius da laifin kashe budurwarsa, Reeva Steenkamp ba da gangan ba.

Mai shari'a, Thokozile Masipa ta ce dan tseren ya yi ganganci wajen amfani da bindiga, amma kuma ta ce masu shigar da kara sun kasa tabbatar da hujjarsu ta cewar da niyya ya kashe ta.

Mr Pistorius ya hakikance a kan cewar bisa kuskure ya harbi Miss Steenkamp, saboda ya yi tsamanin wani ne ya yi masa kutse a gidan nasa.

Za a iya yanke masa hukuncin daurin shekaru 15 a gidan kaso bisa wannan laifin.

Mai shari'a Masipa ta kuma same Mr Pistorius da laifin harbi da bindiga a wani shagon sayar da abinci amma kuma ta wanke shi daga laifuka biyu na amfani da alburushi.