Wani jirgin saman yakin Nigeria ya bace

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Air Marshal Alex Badeh babban hafsan sojojin sama na Najeriya

Ma'aikatar tsaron Najeriya ta ce wani jirgin yakinta na sojin sama samfurin Alpha Jet, ya bata a yankin jihar Adamawa, bayan an tura shi aiki.

A wata sanarwa da darektan watsa labarai na ma'aikatar, Manjo Janar Chris Olukolade ya fitar, ya ce Jirgin da matukansa biyu wanda ke sintiri ya bar Yola ne babban birnin jihar Adamawa da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma'a amma har yanzu ba a ji duriyarsa ba.

Sanarwar ta kara da cewa duk wani kokari na ji daga matukan jirgin ya faskara, yayin da aka shiga kokarin gano su.

Rahotanni sun ce a 'yan kwanakin nan sojojin Nigeria sun yi ta kaddamar da hare-hare kan mayakan Boko Haram wadanda suka kwace wasu garuruwa a yankin arewa maso gabashin kasar.

Karin bayani