Rasha ta kai karin agaji Ukraine

Shugaban Rasha Vladimir Putin na Rasha Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rasha ta fuskanci suka a watan da ya gabata saboda kai kayayyaki irin wannan Ukraine ba da izinin gwamnatin kasar ba.

Kafar watsa labaran Rasha ta rawaito cewa fiye da manyan motoci talatin makare da kayayyakin agaji ne su ka ketara iyakar kasar da Ukraine.

Motocin na dauke ne da kayan abinci, da magunguna da kuma injin bada hasken lantarki, sai dai rahotanni sun ce masu bincike na kasashen waje ba su binciki kayan ba kafin a ketara da su.

Rasha dai ta fuskanci suka a watan da ya gabata, lokacin da mayan motoci dari uku na kayayyakin agaji suka shiga Ukraine ba tare da amincewar hukumar Red Cross ko gwamnatin Ukraine din ba,wadanda ke da alhakin tantance kayyakin kafin a shiga da su.

A bangare guda kuma Amurka ta bi sahun tarayyar turai wajen sake kakabawa Rashar wasu karin takunkumi akan abinda suka kira katsa landan da Moscow ke yi a rikicin Ukraine.

Tun da fari shugaba Vladimir Putin na Rasha yace karin takunkumin zai janyo koma baya a kokarin wanzar da zaman lafiya a Ukraine inda yace watakil wasu ne ba sa farin ciki da dorewar zaman lafiya a Ukraine.