'Yan Najeriya na kokawa a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu 'yan Najeriya da rikicin Boko Haram ya tilasta wa gudun hijira

'Yan Najeriya da ke gudun hijirar fadan Boko Haram a garin Fotokol na Kamaru na cikin halin kaka-ni-kayi.

'yan gudun hijirar da suka fito daga garin Gamborun Ngala sun ce ba su da kudi da abinci.

Kuma sun ce ba su da damar zuwa su yi aiki a garin na Fotokol domin samun kudi, saboda hukumomin Kamaru na cewa ba su da takarda.

Sai dai Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta nanata cewa tana shirin dawo da su Najeriya.

Amma za ta kai masu kayan abincin kamar yadda shugaban Hukumar na shiyyar Arewa maso gabashin kasar Muhammad Kanar ya ce.

A kwanakin baya ne dai 'yan kungiyar Boko Haram suka kwace garin Gamborun Ngala lamarin da ya sa daruruwan mutane tserewa zuwa wasu garuruwa a Najeriya da wajenta.

Karin bayani