Australia za ta bi sahun yaki da 'yan IS

Hakkin mallakar hoto a

Firaministan Australia Tony Abbot ya ce kasarsa za ta aike da dakaru 600 da jirgin yaki zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa, don taimakawa wajen yakar kungiyar ISIL mai da'awar kafa kasar musulunci.

Mr Abbott ya ce matakin ya biyo bayan amincewar Firaministan kasar Iraqi da kuma bukata ta musamman daga Amurka .

Amma ya ce abu mafi muhimmanci shine a samu damar rage tasirin ayyukan kungiyar masu tada kayar bayar, yana mai cewa sare kan dan kasar Birtaniyar da suka yi ya nuna irin ta'asar su.

Karin bayani