An kirkiro memori mafi girma a duniya

Hakkin mallakar hoto SANDISK
Image caption A cikin shekaru goma kamfanin ya kara girman memorin sau 1,000

Kamfanin SanDisk da ya kware wajen kirkiro ma'ajiyar sauti ko hotuna da sauran abubuwa ta zamani wato memory card ya kirkiro mafi girmaa duniya.

Sabuwar ma'adanar tana iya daukar gigabyte 512(GB), wanda kafin samar da wannan nau'i babu wadda ke da wannan girma.

Katin wanda girmansa kamar na kan sarki ne na wasika za a sayar da shi akan dala 800 ko fan 490.

Kamfanin ya kirkiro da wannan sabuwar ma'adana ce bayan da ya kirkiro mai daukar megabyte 512(MB) shekaru goma da suka wuce.

Kwararrun da suka yi wannan kirkira suna ganin nan gaba za a iya samar da wadda za ta dauki abubuwa masu yawan terabyte biyu (TB), wato 2,000GB.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Memorin na iya daukar hoton bidiyo na kusan sa'oi talatin.

An dai kirkiro da wannan sabuwar ma'adana ce domin amfanin masu shirya fina-finai a samfurin 4k.

Samfurin fim na 4k ya linka HD inganci har kashi hudu, wanda hakan ya sa ake bukatar ma'adanar da ke da gurbi mai yawan gaske a aikinsa.

Wannan sabuwar ma'adanar (memory card), za a iya amfani da ita a na'urar daukar hoto samfuri daban-daban.

Ma'adanar wato memorin na iya daukar hoton bidiyon da yawansa na kai na kusan sa'oi talatin.