Boko Haram: Ana karkatar da tallafi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai sama da 'yan gudun hijirar rikicin Boko Haram dubu 429 a sansanonin Najeriya inji NEMA.

Wasu 'yan gudun hijirar rikicin Boko Haram sun yi zargin cewa ana karkatar da kayan agajin da ake kai musu.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar a Mubi ta Adamawa da Marte a Borno sun ce abin da ke isa garesu bai wuce kashi 20 cikin dari na kayan ba.

Gwamnatoci da hukumomi da kuma daidaikun jama'a ne ke bayar da kayan tallafi ga 'yan gudun hijirar a sansanoninsu a jihohin Adamawa da Borno da Gombe.

Sai dai shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, na shiyyar arewa maso gabas Muhammad Kanar, ya ce a saninsu kayan na isa ga mutanen.

Amma kuma shugabar kungiyar bayar da tallafi ta Yadoma and Bukar Mandara Care Foundation daya daga cikin kungiyoyi masu bayar da agaji Hajiya Yadoma ta ce akwai alamun gaskiyar zargin.

Karin bayani