Cameron zai je Scotland kamfe

Firaminstan Burtaniya David Cameron Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karo na biyu cikin mako guda da Cameron ke zuwa yankin Scotland

Firaministan Burtaniya David Cameron, zai koma yankin Scotland don janyo ra'ayin jama'a da su kada kuri'ar rashin amincewa da neman 'yancin cin gashin kan yankin daga Burtaniyar.

Wannan ne karo na biyu cikin mako guda da ya ke zuwa yankin gabannin zaben rabe gardamar da ake shirin yi ranar Alhamis.

Sai dai jagoran jam'iyyar da ke neman 'yancin gashin kan yankin, Alex Salmond, ya yi watsi da yunkurin Mr Cameron wanda ya bayyana a matsayin tsoro.

Mr Salmond ya ce kuri'ar wata dama ce ta sau daya a rayuwa a don haka ya bukaci masu kada kuri'a da su ba da gagarumar gudummawa don cimma wannan burin.

Ya yin da alamu ke nuna cewa bambancin da ke tsakanin masu goyon baya da wadanda basa goyon baya bai da yawa sosai, sarauniya Elizabeth ta ce tana fatan mutane zasu yi tunani mai zurfi game da makomar yankin lokacin da zasu kada kuri'unsu a ranar Alhamis.