David Cameron ya sake komawa Scotland

David Cameron Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption David Cameron

Firayim Ministan Birtaniya, David Cameron ya kai ziyara ta karshe yankin Scotland don jan-ra'ayin al'ummar yankin da ka da su goyi bayan ballewa daga Birtaniya, yana gargadin cewa har jikokinsu sai sun yi da-na-sani idan suka balle.

Sai dai a bangare guda, Babban Ministan yankin Scotland, Alex Salmond, ya ce baiwa yankin 'yanci zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin al'umma.

Mr Salmond yayi zargin cewa da gangan ake tsorata mutane, domin su ki amincewa.

A ranar Alhamis mai zuwa ne ake sa ran kada kuri'ar raba-gardamar.