Ebola ta zama babban bala'i ga bil adama

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Likitoci da dama sun rasu sakamakon cutar Ebola

Hukumar lafiya ta duniya ta ce annobar cutar Ebola a yankin yammacin Afrika abu ne da ba a taba ganin irinsa ba a zamanin.

Hukumar ta ce cutar na yin barazanar haddasa bala'i ga bil adama.

Wani babban jami'in hukumar lafiya ta duniya, Bruce Aylward ya ce ana bukatar matakin gaggawa idan ana son rike yawan mace-mace daga annobar mai karuwa cikin hanzari a kan dubbai.

Kawo yanzu mutane kusan dubu 2 ,500 ne suka mutu sakamakon cutar.

Kungiyar bayar da agajin likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta ce lamarin ya fi karfinta, a inda a Liberia majinyata ciwon na Ebola ke kai kansu asibitoci domin gudun shafar iyalansu.