'Ma'aikacin banki ya sace naira biliyan 6'

Hakkin mallakar hoto EFCC
Image caption EFCC ta ce har yanzu ba ta kama kowa

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria, EFCC ta na neman wani ma'aikacin banki ruwa a jallo bisa zargin sace dala miliyan 40 watau fiye da naira biliyan shida a bankin da yake aiki.

Hukumar EFCC ta ce, Godswill Oyegwa Uyoyou wanda masannin na'urar komfuta ne, ya sace kudin ne a bankin da yake aiki.

Bayanai sun nuna cewar Mr Uyoyou ya hada baki da wasu mazambata suka shiga bankin a ranar Asabar suka yi satar a lokacin da sauran ma'aikata ba sa zuwa ofis.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya ce kawo yanzu ba a kama ko daya daga cikin mutanen da ake zargi da yin zambar ba.