An yi wa kifi tiyata

Hakkin mallakar hoto Lort Smith Animal Hospital
Image caption Kifin ke nan bayan da aka gama yi masa tiyatar mai hadarin gaske

Wani kifi mai launin zinare (Goldfish), da aka yi wa tiyata mai hadarin gaske don cire masa wani kurji a kwakwalwarsa yana murmurewa.

An yi wa kifin mai suna George, wanda mai shi take zaune a birnin Melbourne na Australia, allurar kashe jiki kafin a yi masa tiyatar da aka biya dala 200 kusan Naira dubu 32.

Dokta Tristan Rich wanda ya yi wa kifin tiyatar ya ce, yanzu kifin na murmurewa sosai bayan cire masa kurjin da ya fito masa a ka.

Likitan ya ce, kurjin da ya fito wa kifin (George) yana girma ne sannu-sannu, kuma ya fara shafar lafiyarsa.

Likitocin dabbobi sun ce yanzu kifin mai shekara goma zai iya ci gaba da rayuwa tsawon wasu shekaru 20.

Hakkin mallakar hoto Lort Smith Animal Hospital
Image caption George ke nan bayan an yi masa allurar kashe jiki

An dai bai wa mai kifin zabin ko dai a yi masa tiyata ko kuma a sanya shi barci.

Amma matar ta ce ta yadda a jarraba yi masa tiyatar mai hadarin gaske.

Dokta Rich wanda ya dauki minti 45 wajen yi wa kifin aiki, ya ce nan gaba kadan za a sallame shi daga asibiti.