Ebola: Obama ya roki kasashen duniya

Hakkin mallakar hoto na
Image caption Obama ya ce duniya ta san hanyar dakile Ebola, kuma ya kamata ta yi hakan yanzu domin ceto rayuka

Shugaba Obama ya yi kira ga kasashen duniya da su hanzarta daukar matakan da suka dace domin kare bazuwar annobar Ebola a Afrika ta Yamma.

A lokacin da ya ke jawabi a cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Amurka a Atlanta, Obama ya ce idan ba a dakile cutar ba dubban jama'a za su iya kamuwa.

Haka kuma annobar daga nan za ta iya zama barazana ga duniya baki daya.

Wani janar na sojin Amurkan da zai jagoranci tawagar sojojin kasar a yankin na Yammacin Afrika.

Amurkan za ta kuma samar da hanya ta jiragen sama domin aikawa da ma'aikatan lafiya da kayayyaki Arfika ta Yamman cikin hanzari.

Karin bayani